logo

HAUSA

Shugabannin Kasashe Da Hukumomin Duniya Sun Taya Sinawa Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Gargajiya

2024-02-10 15:32:43 CMG Hausa

Shugbannin kasashe da yankunan duniya da jami’ai da shugabannin hukumomin kasa da kasa sun aike da wasiku ko sakonni ga shugaba Xi Jinping na kasar Sin, domin taya Sinawa murnar shiga sabuwar shekarar Loong.

Cikin sakonsa, shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya ce yana yi wa Sinawa fatan samun farin ciki da koshin lafiya, yana mai cewa, Senegal za ta ci gaba da tsayawa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Shi kuwa shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera cewa ya yi, sabbin nasarorin da Sin ta samu ta hanyar zamanantar da kanta za su kawo sabbin damarmaki ga duniya da sabuwar fata ga kasashe masu tasowa da dama, da samar da karin taimako ga al’ummar Afrika ta Tsakiya wajen cimma burikansu. Ya kara da cewa, a shirye Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya take ta hada hannu da kasar Sin wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya mai inganci.

A nasa bangare, sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya ce a karon farko, ranar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin ta shiga kalandar hutu ta MDD, yana mai bayyana godiya ga kasar Sin da al’ummarta sakamakon goyon bayan da suke ba majalisar da goyon bayan huldar bangarori daban daban da ma ci gaban duniya. (Fa’iza Mustapha)