Shagalin Bikin Bazara Na Taya Masu Kallo A Fadin Duniya Maraba Da Sabuwar Shekarar Loong
2024-02-09 23:20:21 CRI
Yau Jumma’a, ita ce jajibirin sabuwar shekarar Loong bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin. Da misalin karfe 8 na dare agogon Beijing, aka fara gabatar da shagalin Bikin Bazara na CMG ga masu kallo a fadin duniya.
An shirya babban dandalin gabatar da shagalin ne a birnin Beijing, yayin da aka shirya wasu kananan dandamali a Shenyang na lardin Liaoning da birnin Changsha na lardin Hunan da Xi’an a lardin Shaanxi da Kashgar dake jihar Xinjiang.
Shagalin wanda aka shafe shekaru 41 a jere ana gabatar da shi, na kunshe da shirye-shirye daban daban da suka hada da wake-wake da raye-raye da wasannin dabo da na kasada da kokawa da wasannin kwaikwayo da sauransu, wanda ke sanya masu kallo cikin yanayi na annashuwa da farin ciki da murna. A bana, jigon shagalin shi ne, ba daidaikun mutane damar hawa dandali domin gabatar da wasanni.
A yau, CMG ya hada hannu da kafofin yada labarai sama da 2100 a kasashe da yankunan 200 a fadin duniya, domin watsawa da bayar da rahotannin shagalin. Sama da manyan allunan kallo a kasashe 49 da birane 90 a fadin nahiyoyi 6 ne suka gabatar da shagalin a wuraren da jama’a kan taru. (Fa’iza Mustapha)