logo

HAUSA

Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin Ya Haskaka Gasar Wasan Kwallon Gora Kan Kankara Ta Arewacin Amurka

2024-02-09 21:12:27 CMG Hausa

A jajibirin sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin ko Bikin Bazara, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG ya tallata shirin talibijin na murnar sabuwar shekarar, yayin gasar wasan kwallon gora kan kankara na arewacin Amurka a birnin New York.

Sama da Amurkawa 10,000 ne suka kara sanin yanayin murnar Bikin Bazara na kasar Sin, inda su ma suka yi maraba da zuwan sabuwar shekarar dabbar Loong.

A wannan lokaci, daraktan CMG Shen Haixiong, ya gabatar da jawabi ga Amurkawa masu sha’awar wasan kwallon gora kan kankara ta kafar bidiyo, inda a madadin CMG, ya yi musu fatan samun farin ciki da tsawon rai da koshin lafiya.

Shi ma jakadan Sin a Amurka, Xie Feng, ya yi wa kowa fatan samun farin ciki da lafiya a shekarar Loong. (Fa’iza Mustapha)