logo

HAUSA

An kawata wurin sakataka na London Eye albarkacin murnar bikin bazara

2024-02-09 10:13:22 CMG Hausa

A wani bangare na murnar bikin bazara, a jiya Alhamis, an kawata wurin yawon shakatawa na London Eye dake zama daya daga cikin manyan alamomin Buritaniya da launukan ja da kuma zinare, launuka masu kyau da aka saba amfani da su a bikin Bazara, wanda aka fi sani da sabuwar shekara ta kasar Sin.

A cikin tsananin sanyi, mutane sun tsaya suna kallon yadda na’urar dake kudancin kogin Thames ke juyawa, don shaida yadda aka sauya fitilun dake jikinta, don murnar bukukuwan bazara.

Shugaban kamfanin Merlin Entertainment, kamfanin da ya shirya wannan shagali Scott O'Neil, ya bayyana cewa, bikin kunna fitilun, wanda kungiyar Sinawa mazauna birnin London wato Chinatown da London Eye suka gudanar, lamari ne na yau da kullum da aka saba yi duk bikin sabuwar shekara ta kasar Sin tsawon shekaru da dama. An shirya bikin ne, don zama na musamman a wannan shekara, dake zama shekarar dabbar Loong.

O'Neil ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua fahimtarsa game da ma'anar musamman kan dabbar Loong, wadda ke nufin aminci, ci gaba da kuma neman wani abu mai ban mamaki. (Ibrahim Yaya)