logo

HAUSA

Bikin Bazara Dake Da Matukar Muhimmanci A Zaman Rayuwar Sinawa

2024-02-09 11:55:28 CMG Hausa

 

Yanzu haka Sinawa suna murnar bikinsu na gargajiya da ake kira “Chun Jie”, wato Bikin Bazara a Hausance.

Bikin bazara biki ne mafi muhimmanci ga yawancin Sinawa, a cikin bukukuwansu daban daban na duk shekara. Ana wannan biki ne don murnar sabuwar shekara a bisa kalandar gargajiyar kasar.