logo

HAUSA

Kakakin Soji: Harin jirgin yakin Amurka maras matuki a Iraki ya ingiza kawo karshen kawancen aikin soji da Amurka ke jagoranta

2024-02-09 09:37:51 CMG Hausa

Gwamnatin Iraki ta fada jiya Alhamis cewa, harin da jirgin yakin Amurka mara matuki ya kai a gabashin birnin Bagadaza da yammacin Laraba ya sanya gwamnatin Iraki matukar bukatar kawo karshen ayyukan dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta.

Jirgin dai mara matuki ya yi ruwan bama-bamai kan wata motar jigilar harkar wasannin ta dakarun Hashd Shaabi a unguwar al-Mashtal, inda ya kashe a kalla mutane uku, ciki har da Abu Baqir al-Saadi, kwamandan Kataib Hezbollah, wata kungiya mai dauke da makamai da Iran ke marawa baya a Iraki mai alaka da dakarun Hashd Shaabi.

Kakakin sojan firaministan kasar Iraki Yahya Rasoul, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, sojojin Amurka sun sake yin wani kisan gilla a tsakiyar wata unguwa a birnin Bagadaza.

Rasoul ya ce, "Wannan ta’adin ya sa gwamnatin Iraki, fiye da kowane lokaci, ke bukatar kawo karshen aikin kawancen kasa da kasa, wanda ya zama sanadin rashin zaman lafiya ga Iraki." (Yahaya)