logo

HAUSA

Wakilin Sin: Sin Za Ta Yi Iyakacin Kokarin Marawa AntÓNio Guterres Baya Da Ayyukan MDD

2024-02-08 11:30:17 CGTN HAUSA

Jiya Laraba, wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya ce, Sin za ta ci gaba da marawa António Guterres baya da ayyukan MDD, ta yadda za ta hada kai da sauran kasashe don karin taka rawa ga sha’anin duniya na tabbatar da adalci.

Zhang Jun ya bayyana a gun taron shekara-shekara na yin bayani kan muhimman ayyuka na MDD cewa, a karkashin jagorancin António Guterres, MDD ta tinkari kalubaloli da yanayin ko ta kwana yadda ya kamata, da kuma dukufa kan wanzar da zaman lafiya da ingiza bunkasuwa mai dorewa a duniya, Sin na jinjinawa kokarin da yake bayar. A sabuwar shekara kuwa, ana fuskantar kalubaloli irin daban-daban, dalilin da ya sa ake bukatar majalisa mai karfi. Sin tana yin kira ga bangarori daban-daban da su hada kansu don magance wahalhalu tare, da ma goyon bayan jagorancin da majalisar za ta bayar cikin harkokin duniya.

Zhang Jun ya kara da cewa, muradun tsarin mulkin MDD ba zai canja ba duba da sauyawar yanayin duniya. Dole ne a yi watsi da yin jayayya, kuma a nace ga kulla hadin gwiwa. Kana, kasashe mafi karfi suna da nauyi mafi girma a wuyansu, ya kamata su ba da gudunmawarsu yadda ya kamata. (Amina Xu)