logo

HAUSA

An sako jami’in Kamaru da aka yi garkuwa da shi

2024-02-08 11:40:19 CMG Hausa

A jiya Laraba ne gwamnan yankin arewa maso yammacin kasar Kamaru da ke fama da rikici Adolph Lele L'Afrique ya bayyana cewa, an sako wani jami’in kasar da aka yi garkuwa da shi a yammacin ranar Talata a yankin.  

An yi garkuwa da Nicholas Nkongho Manchang, Hakimin Bamenda II, a wani reshen yankin ne tare da wasu mutane biyar a lokacin da suke kan hanyarsu ta halartar wani biki a hukumance.

An sako jami’in ne biyo bayan aikin soji da aka yi, sa’o’i hudu bayan da aka yi garkuwa da shi, a cewar L'Afrique.

Sauran mutane biyar da aka yi garkuwa da su har yanzu suna hannun masu garkuwan, kuma yana da muhimmanci da jama'a su ci gaba da baiwa jami'an tsaro bayanan da za su kai ga sako su, a cewar L'Afrique yayin da yake jagorantar wani biki a Nkambe, wani gari a yankin.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin sace mutanen. (Yahaya)