logo

HAUSA

Messi bai buga wasan sada zumunta tsakanin Inter Miami CF da kungiyar Hong Kong ba

2024-02-08 21:43:08 CMG Hausa

Lionel Messi bai buga wasan sada zumunta da aka yi a tsakanin Inter Miami CF da kungiyar Hong Kong ba, wadda kungiyar Inter Miami CF ta doke ta Hong Kong da ci hudu da daya. Bayan kammala wasan, mai horas da kungiyar Inter Miami CF Gerardo Martino ya bayyana cewa, kungiyar ce ta yanke wannan kudurin bisa yanayin lafiyar dan wasan.

A ranar 4 ga wannan wata, masu sha’awar wasan kwallon kafa kimanin dubu 40 suka taru a babban filin wasa na Hong Kong, domin ganin Lionel Messi. Amma shaharerren dan wasan Inter Miami CF bai fito a cikin jerin sunayen ‘yan wasan kungiyar da za su fara buga wasan ba, Sergio Busquets da Jordi Alba ne kawai suka shiga wasan a minti na 62. A duk tsawon wasan, Lionel Messi ya zauna a benci. Shi ma mashahurin dan wasan kasar Uruguay Luis Suárez bai buga wasan ba, inda ya motsa jiki na dan wani lokaci a gefen fili.

Kafin wasan, bangaren yankin Hong Kong ya bada labarai ko sanarwa da dama game da wannan wasa, babu shakka mashahurin dan wasa Messi ya fi jawo hankali sosai. A yayin wasan, duk da yadda masu sha’awar wasan kwallon kafa suka rika kiran sunan Messi, amma ba su cimma burinsu na ganin Messi ya buga wasan ba. A yayin da aka kusa kammala wasan, wasu ‘yan kallo sun fara ficewa daga filin wasan, suna kuma daga murya kan a “mayar musu da kudin tikitinsu”.

A yayin taron manema labaru da aka gudanar bayan kamala wasan, mai horaswa Gerardo Martino ya shaidawa ‘yan jarida cewa, ya san masu sha’awar wasan kwallon kafa ba su ji dadin rashin bayyanar Messi da Suárez a wasan ba, amma an tsaida wannan kuduri ne domin ‘yan wasan biyu sun ji rauni. Ya ce, ita ma kungiyar tana son ‘yan wasan su buga wasan koda na dan wani lokaci ne, amma idan an yi hakan, za su iya fuskantar hadari. Game da raunin da Messi ya ji kuwa, Martino ya bayyana cewa, dan wasan kasar ta Argentina ya gamu da kumburi a jijiyarsa, na tsawon lokaci, Martino yana fatan masu sha’awar kwallon kafa za su fahimci wannan matsala.

A wasan da kungiyar Inter Miami CF ta buga da kungiyar Al-Nassr FC ta kasar Saudiyya, Messi ya shiga wasan ana kusa da kammalawa. Bayan da kungiyar Inter Miami CF ta iso yankin Hong Kong a ranar 2 ga wannan wata, Martino ya bayyana cewa, za a yi la’akari da lokacin da ya kamata Messi ya buga wasan bisa yanayin rauninsa. Messi ya yi atisaye kadan, amma bai shiga babban atisaye da ‘yan wasan suka yi cikin rukuni a ranar 3 ga wannan wata ba.

Tambayar da aka yi masa a gun taron manema labaru cewa, ko kungiyar ta san Messi ba zai buga wasan ba tun tuni, Martino ya bayyana cewa, kungiyar tana bibiyar raunin da Messi ya ji, kuma kungiyar ta tsaida wannan kuduri ne a safiyar ranar 4 ga watan.

A ranar 5 ga wata, shugaban hukumar kula da harkokin al’adu da wasanni da yawon shakatawa ta gwamnatin yankin Hong Kong Yang Runxiong da jami’in kula da wasanni Huang Desen sun gana da ‘yan jarida game da wannan batu. Mr Yang ya bayyana cewa, kafin wasan, bangaren shirya wasan ya tabbatar da cewa, Messi zai buga wasan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci na wasan, amma daga bisani sai aka gano cewa, Messi bai shiga wasan ba. Gwamnatin yankin Hong Kong ta sha tuntubar bangaren shirya wasan don nuna ganin an sanya Messi a wasan. Amma sai zuwa minti 10 kafin kammala wasan, bangaren shirya wasan ya tabbatar da cewa, Messi ba zai iya buga wasan ba saboda rauni da ya ji.

Game da wannan batu, Mr Yang ya bayyana cewa, wannan wasa ne dake jawo hankalin jama’a sosai, kana gwamnatin yankin Hong Kong ta nuna goyon baya sosai wajen sa kaimi ga gudanar da wasan. Ban da samar da filin wasan, an samar da gudummawa a fannoni daban daban, amma sharadi daya shi ne Messi zai buga wasan na a kalla minti 45. Yang ya jaddada cewa, ya kamata bangaren shirya wasan ya dauki alhakin yin bayani game da hakikanin batun ga jama’a da masu sha’awar wasan. Yana mai cewa, gwamnatin yankin Hong Kong za ta koyi darasi daga wannan batu, da kara kyautata ayyukansu a nan gaba.