logo

HAUSA

Babban jami’in wanzar da zaman lafiya na MDD ya bukaci kungiyar M23 da ta dakatar da kai hare-hare a gabashin DRC

2024-02-08 11:41:13 CMG Hausa

Mukaddashin babban sakataren MDD mai kula da ayyukan wanzar da zaman lafiya Jean-Pierre Lacroix, a jiya Laraba ya yi kira ga kungiyar masu tawaye na M23 da su gaggauta tsagaita bude wuta a gabashin jamhuriyar demokradiyyar Kongo (DRC).

Ya bayyana hakan ne a wata ganawa da manema labarai bayan ziyararsa a gabashin kasar tsakanin ranar 2 zuwa 5 ga wata, musamman garuruwan Goma, Beni da Bukavu, inda matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa sakamakon yakin da ake yi tsakanin sojojin kasar da kungiyoyin masu dauke da makamai ciki har da M23.

Yayin ziyararsa, Lacroix ya tattauna tare da masu shiga tsakani kan kalubalen tsaro, da ci gaba da janyewar Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a DRC (MONUSCO) da kuma hana cin zarafin mata.

A yayin ganawarsa da Janar Dyakopu Monwabisi, kwamandan kungiyar hadin kan kasashen kudancin Afirka (SADC) a DRC, Lacroix ya jaddada muhimmancin hada kai don tallafawa sojojin DRC a yakinsu da kungiyoyin masu dauke da makamai a gabashin DRC. (Yahaya)