logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya na kokarin saukakawa al’ummar kasar matsalolin hauhawar farashin kayan abinci

2024-02-08 09:48:41 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce, za ta bude runbunanta na ajiyar kayan abinci domin saukakawa al’ummar kasar matsalolin hauhawar farashin kayan abinci da ake fuskanta a halin yanzu a kasar.

A lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan fitowa daga zaman farko na taron kwanaki uku da aka shirya da zumma lalubo hanyoyin saukakawa al’umma, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na tarayyar Najeriya Alhaji Mohammed Idris ya ce, gwamnati ba za ta samu natsuwa ba a yanayin al’ummar kasa ke cikin yunwa.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan yada labaran na tarayyar Najeriya ya ci gaba da cewa, gwamnati za ta bi dukkan hanyoyin da suka kamata domin dai tabbatar da ganin an samar da wadataccen abinci kuma mai rahusa ga ’yan Najeriya.

Ya tabbatar da cewa, tuni aka fara zama da masu kamfanonin samar da abinci da ’yan kasuwa domin neman su fitar da kayayyakin da suke da shi a runbunan ajiyar su domin sayarwa ga al’umma a kan farashi mai sauki, yayin da ita kuma gwamnati za ta duba hanyoyin da za ta taimakawa ’yan kasuwar.

“Gwamnati ta lura cewa, akwai abinci a kasar, amma wasu mutane suna amfani da yanayin da ake ciki na tsadar rayuwa da kuma faduwar darajar kudinmu wajen daga farashin kayayyakin abinci, gwamnati ba za ta rungume hannuwan ta bari ’yan Najeriya su ci gaba da fuskantar wahala ba wajen neman abinci, ina son na tabbatar da cewa, da zarar mun kammala wadannan tarurruka namu da muka fara tun daga jiya Laraba, gwamnati za ta fitar da matsayarta, kuma nan ba da jimawa ba za a kawo karshen matsalolin ’yan Najeriya.”

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ne yake jagorantar taron, kuma daga cikin mahalarta taron sun hada gwamnan babban bankin kasar da ministan kudi da mashawarcin shugaban kasa kan sha’anin tsaro da ministan tsare-tsaren tattalin arziki da kuma wasu shugabannin hukumomin gwamnati. (Garba Abdullahi Bagwai)