logo

HAUSA

Tawagar tabbatar da zaman lafiya ta AU ta ziyarci Somaliya don tabbatar da mika mulki cikin kwanciyar hankali

2024-02-08 11:41:57 CMG Hausa

Wata tawaga daga tsarin tabbatar da daidaito na kungiyar Tarayyar Afirka (AUCF), wanda ke inganta ayyukan tabbatar da zaman lafiya na kungiyar AU ta hanyar bin dokokin kasa da kasa, ta ziyarci Somaliya domin karfafa kokarin kare fararen hula gabannin mika mulki.

Tawagar ta AU ta ce, a wani bangare na ziyarar da za ta yi na tsawon mako guda a Somaliya, za ta tattauna da masu ruwa da tsaki daban-daban, da suka hada da jami'an gwamnati, da ATMIS, da MDD, da kungiyoyin fararen hula, domin kara inganta kare fararen hula a lokacin da ake shirin mika mulki. (Yahaya)