logo

HAUSA

Cote d'Ivoire za ta karbi bakuncin bikin al'adun yammacin Afirka karo na farko

2024-02-07 10:58:36 CMG Hausa

Bikin fasaha da al'adu na yammacin Afirka (ECOFEST), wanda shi ne bikin al'adun yammacin Afirka na farko, zai gudana a kasar Cote d'Ivoire daga ranar 28 ga watan Satumba zuwa 5 ga Oktoba, 2024, kamar yadda Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta bayyana.

Taron wanda kungiyar ECOWAS da kungiyar hadin kan tattalin arziki da lamuni ta Afirka ta Yamma (UEMOA) suka shirya, na da nufin inganta al'adun yankin da tabbatar da kyakkyawar mu'ammalar bai daya ta ECOWAS da UEMOA a tsakanin al'ummar yankin. (Yahaya)