logo

HAUSA

Isra'ila ta kai hari da makami mai linzami a yankin Homs na kasar Sham

2024-02-07 10:26:23 CMG Hausa

Isra'ila ta kai harin makami mai linzami kan wasu yankunan da ke tsakiyar lardin Homs na kasar Sham, da tsakar daren Laraba, kamar yadda gidan talabijin din kasar ya rawaito.

Dakarun tsaron saman Sham sun kakkabo tare da lalata makamai masu linzami da dama, yayin da wasu 'yan tsiraru suka sauka a cikin karkarar Al-Qusayr, lamarin da ya yi sanadin tashin gobara a yankin.

Kungiyar kare hakkin bil'Adama ta Sham ta ce an ji karar fashewar bama-bamai sau tara a Homs da kauyukanta sakamakon harin. (Yahaya)