Kusan kaso 90 na wadanda suka amsa wata kuri’ar ra’ayin jama’a a duniya, sun ce rikici tsakanin bangarorin Amurka na neman zama jiki
2024-02-07 20:39:16 CMG Hausa
‘Yan cirani na kara shiga tasku yayin da matsalar bambamcin jam’iyya ke kara kamari a Amurka. Ana ci gaba da takkadama tsakanin gwamnatin jihar Texas da gwamnatin tarayyar Amurka kan batun ‘yan cirani, inda wasu ke daukarsa a matsayin “rabuwar kai ta cikin gida”.
Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a a duniya da CGTN ta gudanar ta intanet ta nuna cewa, kaso 86.5 na wadanda suka bada amsa, sun yi ammana cewa fito-na-fito da ake yi tsakanin bangarorin biyu dangane da batun ‘yan ci rani ya kara bayyana gaskiyar cewa jam’iyyun siyasa biyu na Amurka suna kara wasa wukar kishi da juna, kuma tsarin siyasar kasar na kara tabarbarewa.
Batun ‘yan ciranin ya dade da zama wani batu da ake takkadama kansa tsakanin jam’iyyun Repulican da Democrat a Amurka. Domin kaucewa abun da zai taba siyasarsu, har ta kai jam’ iyyun biyu suna turawa juna ‘yan cirani.
Yayin zaben tsakiyar zango na shekarar 2022, ‘yan siyasar jam’iyyar Republican, ciki har da gwamnan jihar Texas, sun yi amfani da motocin safa-safa da jiragen sama wajen kai dubban ‘yan cirani zuwa biranen dake karkashin mulkin jam’ iyyar Democrat.
Nazarin ya nuna cewa, kaso 70.2 na wadanda suka bayar da amsa, sun damu matuka game da karuwar cin zarafi daga gwamnatin Amurka dangane da batutuwan da suka shafi ‘yan cirani, kuma sun yi imanin cewa, jami’an tsaro a kasar sun yi matukar take hakkokinsu.
Dandamalin sassan Turancin Ingilishi da Spaniya da Faransanci da na harshen Rasha da Larabci, na kafar yada labarai ta CGTN ne suka fitar da nazarin, inda masu amfani da yanar gizo sama 11,000 suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’o’i 24.