Kasar Sham ta zargi Amurka da kara kaimi ga sace dukiyar kasarta
2024-02-07 10:16:53 CMG Hausa
Kamfanin dillacin labarai na SANA na kasar Sham ya sanar a ranar talata cewa, sojojin Amurka sun zafafa kai hare-hare don wawushe dukiyar kasar Sham, musamman mai da hatsi.
SANA ta zargi sojojin Amurka da fitar da mai da hatsi daga kasar ta haramtacciyar hanya, tana mai cewa sun yi jigilar tankokin mai da motocin dakon kaya 160 cike da kayan sata zuwa Iraki cikin sa'o'i 24 da suka gabata.
Kamfanin dillancin labaran ya nakalto daga majiya mai tushe a lardin al-Hasakah da ke arewa maso gabashin kasar cewa, ayarin motocin tankokin 84 dauke da mai daga yankin al-Hasakah sun tsallaka kan iyakar al-Mahmoudiyah zuwa sansanoni Amurka dake Arewacin Iraki.
Wani ayarin motocin dakon kaya 76 dauke da alkama da sha'ir daga rumbunan hatsi da mayakan Kurdawa na Syrian Democratic Forces da ke samun goyon bayan Amurka suka kwace, sun tsallaka kan iyakar Al-Walid zuwa Iraki. (Yahaya)