logo

HAUSA

Gwamnonin Najeriya sun kawo shawarar mayar da shirin tallafin rance noma zuwa ma’aikatar gona maimakon babban bankin kasar

2024-02-07 08:57:04 CGTN HAUSA

 

Kungiyar gwamnonin jihohi a tarayyar Najeriya ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta kara azama wajen bunkasa sha’anin noma domin maganin hauhawar farashin kayan abinci da karancinsa a kasar.

Shugaban kungiyar, kuma gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq ne ya bukaci hakan a birnin Abuja lokacin da ya jagoranci wasu daga cikin ’yan kungiyar zuwa ofishin ministan harkokin noma da bunkasa samar da abinci.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.