Mataimakin firaministan Sin ya gana da babban jami'in baitul malin Amurka
2024-02-07 10:08:50 CGTN HAUSA
Mataimakin firaministan kasar Sin, kuma shugaban tawagar kasar Sin kan tattaunawar harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka He Lifeng, ya gana da wata tawaga karkashin jagorancin Jay Shambaugh, mataimakin sakataren harkokin kasa da kasa a ma'aikatar kudi ta Amurka, jiya Talata a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Yayin ganawar, He Lifeng ya yi nuni da cewa, kamata ya yi bangarorin biyu su yi aiki tare, don aiwatar da muhimman shawarwarin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a taron San Francisco, da ci gaba da yin amfani da matakan tattaunawa yadda ya kamata, da zurfafa mu'amala da hadin gwiwa, da samar da daidaito, da daidaita al'amura da raya dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu, da kara kawo alheri ga kamfanoni da jama'ar kasashen biyu.
A nasa bangaren Jay Shambaugh ya bayyana cewa, ya zo kasar Sin ne, don halartar taro na uku na rukunin tattaunawar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka. (Ibrahim Yaya)