logo

HAUSA

An kaddamar da taron zuba jari kan masana’antar ma’adinai na Afirka karo na 30 a Afirka ta Kudu

2024-02-06 10:07:50 CMG Hausa

An gudanar da bikin kaddamar da taron zuba jari na masana’antar ma’adinai na Afirka karo na 30 a babban dakin taron kasa da kasa dake birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu a jiya, da nufin ba da goyon baya da karfafa sauye-sauye da sabbin fasahohi a masana'antar hakar ma'adinai ta Afirka, don bunkasa ci gabanta da samun ci gaba mai dorewa.

Taken taron na wannan karo shi ne “Yin kokarin kirkiro sabuwar makomar masana’antar hakar ma’adinai ta Afirka”. Taron na tsawon kwanaki hudu, zai gudana ne daga ranar 5 zuwa 8 ga wannan wata.

Manyan jami’an gwamnatocin kasashen Afirka da masu zuba jari a fannin hakar ma’adinai da ‘yan kasuwa fiye da dubu 8 sun halarci taron, kuma shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Cyril Ramaphosa ya gabatar da jawabi a yayin bude taron. (Zainab)