logo

HAUSA

Me Ya Sa Babur Da Kasar Sin Ta Samar Yake Samun Karbuwa

2024-02-06 15:55:14 CGTN HAUSA

DAGA MINA

Kwanan baya, wani bidiyon da ke nuna yadda wani tsohon Ba-Amurke yana tuka wani babur mai kafa 3 mai amfani da wutar lantarki da Sin ta kera, a kan hanyarsa ta zuwa hukumar yiwa ababen hawa rijista, ya karade kafafen sada zumunta a kasashen yamma. Mutane da dama na mamakin irin wannan babur, inda suka yi fatan sayen guda daga kasar Sin.

An ba da labari cewa, tun farkon wannan shekara, adadin Amurkawa da suka sayi irin wannan babur daga kasar Sin ta Intanet, ya ci gaba da karuwa.

Me sa ya? Dalili shi ne, kasar Sin ta hade masana’antun samar da kaya a wuri guda don hada karfinsu na samar da kaya mafi inganci.

Misali, yankin masana’antun samar da motoci masu amfani da wutar lantarki na birnin Xishan a lardin Jiangsu dake gabashin Sin ne, ya kera wannan babur da ya shahara matuka a shafin Intanet. A matsayinsa na cibiya mafi girma dake samarwa da kuma nazarin motoci masu amfani da wutar lantarki da sassan na’urorinsu, yankin ya kunshi kamfanoni masu amfani da fasaha ta zamani 23, suna kuma samun lambobin kira kimanin 200 a kowace shekara.

Sana’ar samar da babur, tana shaida ci gaban sana’o’in kasar Sin, wanda hakan ya sa kasar ta iya samar da kayayyaki masu inganci ga kasuwar duniya.

Abokai, ko ku ma kuna son ku sayi irin wannan babur din daga kasar Sin? (Mai zane da rubutu: MINA)