Sin ta yi kira da a sassauta yanayin yankin Gabas ta Tsakiya
2024-02-06 14:21:18 CMG Hausa
A baya-bayan nan ne sojojin kasar Amurka suka kai hare-hare ta sama kan wasu wurare a kasashen Iraki da Syria a matsayin martani ga harin da aka kai kan sansanonin sojin Amurka dake kasar Jordan a ranar 28 ga watan Janairu. A jiya, kwamitin sulhun MDD ya gudanar da taron gaggawa game da wannan batu, inda zaunannen wakilin Sin dake MDD Zhang Jun ya bayyana cewa, matakan soja da kasar Amurka da sauran kasashe suka dauka, na haifar da sabon rikici a wannan yanki da kuma kara rura wutar rikicin. Yanzu yanayin yankin Gabas ta Tsakiya ya tsananta, abu mai muhimmanci ga kasa da kasa shi ne sa kaimi ga sassauta yanayin da magance tsananta rikicin.
Kasar Sin ta bayyana cewa, Amurka ta kai hare-hare ta sama a wurare da dama a Syria da Iraki, lamarin da ya yi sanadin hasarar rayuka da dama, kuma hakan ya sabawa ikon mallaka da cikakken yankin kasashen biyu. Amurka ta yi ikirarin cewa, za a ci gaba da matakan soji da abin ya shafa, kasar Sin ta nuna matukar damuwa kan hakan, tana kuma adawa da ayyukan da suka saba wa kundin tsarin mulkin MDD, da kuma keta hurumin kasa da tsaron wasu kasashe.
Kasar Sin ta bayyana cewa, babban dalilin da ya sa ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya cikin 'yan watannin da suka gabata shi ne, ba a aiwatar da shirin tsagaita bude wuta da kuma dakatar da yaki a zirin Gaza ba. (Zainab)