logo

HAUSA

NAFDAC:Kaso 50 na magungunan da ake shigar da su Najeriya na jabu ne

2024-02-06 09:19:03 CGTN HAUSA

 

Hukumar tabbatar da ingancin abinci da magunguna a tarayyar Najeriya, wato NAFDAC ta bayyana cewa kaso 50 na magungunan da ake shigar da su kasar ba su da inganci.

Darakta janaral na hukumar Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta tabbatar da hakan a birnin Abuja yayin wani taron masu ruwa da tsaki, da masu tsara manufofi da kuma wakilan hukumomin tabbatar da doka, inda ta ce, akasarin shedar da ake likawa a jikin magungunan na jabu ne.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.