logo

HAUSA

Ofishin gwamnan da’irar birnin Yamai ya tabbatar da bullowar cutar murar tsuntsaye H5N1

2024-02-06 09:30:56 CGTN HAUSA

A jamhuriyyar Nijar an gano cutar murar tsuntsaye ta H5N1 a cikin wani gidan kiwon kaji dake unguwar Plateau dake birnin Yamai. Hukumonin Yamai sun tabbatar da hakan cikin wata sanarwar ofishin gwamnan Yamai ta ranar 30 ga watan Janairun shekarar 2024.

Daga birnin Yamai abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da rahoto.