logo

HAUSA

Yawan furannin da ake sayarwa a Sin ya karu matuka domin murnar zuwan Bikin Bazara

2024-02-05 15:32:37 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, barka da war haka. A halin yanzu, yawan furannin da ake sayarwa a sassan kasar Sin ya karu matuka domin murnar zuwan Bikin Bazara, biki mafi muhimmanci a kasar Sin. Mutane suna son kawata gidajensu domin maraba da zuwan sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, yayin da suke fatan samun wadata da jin dadin zama cikin shekara mai zuwa.