logo

HAUSA

’Yan Nijar dake zaune a Cote d’Ivoire sun bayyana ra’ayoyinsu kan fitar Nijar daga kungiyar CEDEAO tare da fatan mafita ta sulhu

2024-02-05 10:19:42 CMG Hausa

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar a ranar Lahadi 28 ga watan Janairun shekarar 2024, kasar Nijar tare da kasashen Burkina Faso da Mali sun bayyana ficewarsu daga cikin kungiyar CEDEAO ko ECOWAS. Kungiyar dake kunshe da kasashe 15 kafin fitar kasashen AES. Shin ko yaya ’yan Nijar da ke zaune a kasar Cote d’Ivoire suka ji da wannan mataki?

Wakilinmu, Mamane Ada ya tuntubi wasu daga cikinsu dake birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire ga abin da suke cewa: 

“Assalam Alaikum waramatullahi wabarakatu rediyo Sin barka ku da safiya da fatan kowa na cikin koshin lafiya. Kma mun gamsu da cewar da Nijar ta fita cikin CEDEAO, mun ji dadi sosai, insha Allahu, Allah ya kama mana.”

“Gidan rediyo Sin barka ku da yau ina muku fatan alheri kuna tare da naku na yau da kullum, mai saurarenku a kowane lokaci Sale Leko, wanda yake nan cikin Cote d’Ivoire. To a gaskiya ni na yi goyon baya sosai da kasarmu da Nijar, da Mali da Burkina suka fita daga cikin CEDEAO, zamanmu lafiya lau iyakaci dai mutum ya san abin da yake yi, ya bi dokoki, lafiya lau za mu zaunawa insha Allahu, babu wata matsalar da za ta samu.”

“Da fatan ana cikin koshin lafiya, e hulda tsakaninmu ’yan kasar Cote d’Ivoire babu wata matsala, babu wata matsala. Al’ummar Nijar, al’ummar Cote d’Ivoire babu matsala tsakaninmu da su, babu komi sai zaman lafiya, kuma babu wanda aka takurama.”

“Sunana Issoufou Ibrahim Bako dan Nijar mazaunin kasar Cote d’Ivoire, yadda muka ji da wannan al’amari, al’amari ne wato idan ka ji shi a mazauninka na kasar Cote d’Ivoire, ko kuma wata kasa wanda babu ka a cikin Nijar, dole ka ji babu dadi. Amma ni dai fatana shi ne wato kasashe da su da ECOWAS su samu sulhu a zauna bisa tebur, ni a nawa tunani idan Allah ya yarda kwanaki na tafe za’a samu mafita tsakanin wato ECOWAS da wato kasashen nan guda uku na AES.”

Mamane Ada, sashen Hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.