logo

HAUSA

An nuna bidiyon dandanon liyafar bikin bazara ta CMG a gasar wasan kwallon gora ta Rasha

2024-02-05 14:09:14 CGTN HAUSA

 

Ran 2 ga wata, an nuna bidiyon da CMG ya shirya game da liyafar murnar sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin a gasar wasan kwallon gora ta Rasha da aka gudanar a filin wasa na Mytishchi dake arewa maso gabashin kasar Rasha, bidiyon ya jawo hankalin ‘yan kallo matuka tare da samun karbuwa

Wasu ‘yan kallo sun bayyana cewa, wannan ne karon farko da suka kalli bidiyon dandanon bikin CMG a gasar wasan kwallon gora na kankara, kuma sun nuna sha’awa tare da gamsuwa matuka. Har ila yau, sun aike da gaisuwar sabuwar shekara ga jama'ar kasar Sin, tare da fatan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Rasha da Sin da al'ummomin kasashen biyu za su karfafa, kuma zumuncin ya dore har abada. (Amina Xu)