logo

HAUSA

An nuna bidiyon dandanon liyafar bikin bazara ta CMG a siniman Amurka

2024-02-05 14:06:18 CGTN HAUSA

 

Daga ran 2 ga wata, an nuna bidiyon da CMG ya tsara don dandanon liyafar murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin a rukunin gidajen sinima na AMC da sauransu, inda za a nuna wannan bidiyo sau fiye da dubu 60 a allunan talabijin 1169.

An watsa wannan bidiyon a manyan birane 8 na Amurka, kafin a fara gabatar da fina-finan, a sa’i daya kuma, an gabatar da shi a zagaye a wurin hutu da sayar da tikiti a cinima.

An ce, an kafa rukunin AMC a shekarar 1920, ya kasance rukuni mafi girma a duniya, dake rike da yawancin kasuwannin cinima a Amurka. Ban da wasu manyan birane da a baya ake gabatar da irin wannan bidiyo a shekarar 2023, a wannan karo kuma, AMC ta kara gabatar da irin wannan bidiyo a biranen Boston, Houston, Dallas da dai sauran birane, abin da ya alamanta cewa, liyafar bikin bazara ta CMG ta kara habaka tasirinta ga masu kallo na Amurka. (Amina Xu)