logo

HAUSA

Shekarar Loong: Kasashen Duniya Na Kara Fahimtar Al’adun Sinawa Duk Da Adawar Kasashen Yamma

2024-02-05 15:39:52 CMG Hausa

Yayin da kasashe da dama ke ci gaba da gudanar da shagulgula don taya Sinawa murna gabanin bikin sabuwar shekarar kasar Sin bisa kalandar gargajiyar kasar, tuni Majalisar Dinkin Duniya ta karrama bikin sabuwar shekarar kasar Sin ko kuma bikin bazarar Sinawa a matsayin bikin da miliyoyin mutane ke murnarsa a duk duniya. Bikin na wannan shekarar ya fada a ranar 10 ga watan Fabrairu, kuma an yi wa shekarar ta 2024 lakabi da shekarar dabbar Loong, dabbar da kasashen yamma suke kira Dragon na kasar Sin.

Kafofin yada labarai na yammacin duniya su kan yi amfani da hoton Dragon mai aman wuta don nuna kyama ga kasar Sin. Don haka kada ku yi mamakin ganin manyan kafafen yada labarai na yamma suna amfani da kanun labarai masu nasaba da "Dragon" da zane-zane don yin ba’a da yada labarai na son zuciya game da kasar Sin a cikin shekarar Loong.

Jaridar “The Economist” ta riga ta wallafa dabbar Dragon mai amayo wuta a doron kasa a bangonta, tare da taken "Mai Gurbata Duniya Mafi Muni." Wannan ikirari ya yi watsi da gaskiyar cewa a tarihi, kasashen Amurka da na Turai su kasance mafi girman al’ummomi masu gurbata muhalli da hayaki carbon tun bayan juyin juya halin masana'antu, yayin da hayakin da kamfanonin kasar Sin ke fitarwa ke kasa da wanda yawancin kamfanonin kasashen yammacin ke fitarwa.

Kasar Sin ta zamani tare da tattalin arzikinta dake karkashin jagorancin tsarin mulkin gurguzu ta riga ta shige gaba a harkar kiyaye muhallin duniya. Mu sani cewa rana ta fito a gabas kuma ta haska duniya gaba daya, kasar Sin ta kasance tamkar “Mai rike da fitilar kwai a cikin duhu yayin da sauran mutane ke laluben mafita” ci gaban kasar Sin “kamar tsawa ce da ta gitta teku, haskenta kawai ake gani amma ta riga ta kai masaukinta”.    

An tsara tattalin arzikin kasar Sin cikin adalci tare da kyakkyawar fatan rayuwa, da matsayin kiwon lafiya mai inganci, da samar da ilimi, kuma yana kan gaba a dukkan ma'aunin farin ciki yayin da abokan hamayyarta suka tsunduma cikin kunci. Sun shagala da haifar da rikice-rikice a duniya, sun zama tamkar dujal tare da halaka dubban rayuka, yayin da kasar Sin ta shagala da tabbatar da zaman lafiya, sulhu da jituwa.

Dabi’ar kasar Sin daidai take da dabi’ar dabbar Loong, tana cike da kwarjini, kwazo, wadata, wanda ba ta da nufin danniya ko mamaya sai dai hadin kai da falsafar cin nasara tare. (Muhammed Yahaya)