logo

HAUSA

WHO ta yi gargadin saurin yaduwar cututtuka da sauro ke haddasawa

2024-02-05 08:26:11 CMG Hausa

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta yi gargadi a kwanan baya cewa, sauyin yanayi ya kara saurin yaduwar zazzabin Dengue da na Chikungunya da sauran cututtukan da sauro ke haddasawa, wadanda za su kara yaduwa a wurare da dama.

Babban jami’in WHO mai kula da dakile da kandagarkin zazzabin Dengue da cututtukan da sauro ke haddasawa ya bayyana wa ‘yan jarida cewa, sauyin yanayi na kara saurin yaduwar cututtukan da sauro ke haddasawa. Bari mu dauki zazzabin Dengue a matsayin misali. Kasashe da yankuna 129 a duniya na fuskantar barazanar yaduwar irin wadannan cututtuka, a cikinsu kuma, wasu kasashe da yankunan 100 ne suke tinkarar yaduwar cututtukan a wasu wurare. A shekarun baya-bayan nan, yawan masu kamuwa da zazzabin Dengue ya karu matuka, daga kimanin dubu 500 a shekarar 2000 zuwa miliyan 5 da dubu 200 a shekarar 2019. Adadin ya kai sabon matsayi a tarihi. Ko da yake barkewar cutar numfashi ta COVID-19 ta haifar da matsala wajen aikin kidayar yawan masu kamuwa da ciwon, amma masu kamuwa da ciwon suna da yawa matuka.

Mene ne zazzabin Dengue? Madam Zhang Chuji, likita ce da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, zazzabin Dengue, wani nau’in cuta ce mai yaduwa da kwayar cutar Dengue ke haifarwa. Cutar ta kan yadu a wurare masu zafi. Wadanda suka kamu da ciwon suna fama da zazzabi mai zafi,da ciwon kai, da ciwon jijiyoyi, har ma da na gwiwa da sauransu. Akwai wani nau’in zazzabin Dengue mai hadari, wato Dengue Hemorrhagic Fever, wanda kan haddasa mutuwa.

Babbar jami’ar WHO mai kula da fasahar dakile da kandagarkin zazzabin Chikungunya da zazzabin Zika ta yi nuni da cewa, tun bayan da aka gano barkewar zazzabin Chikungunya a shekarar 1950 ya zuwa yanzu, kasashe da yankuna 115 ne suka sanar da samun wadanda suka kamu da ciwon. Yanzu haka ciwon yana yaduwa cikin sauri a nahiyar Amurka.

Zazzabin Chikungunya, wani nau’in ciwo ne mai yaduwa da kwayar cutar Chikungunya ke haddasawa. Wadanda suka kamu da ciwon su kan yi fama da zazzabi da ciwon gabobi. Ana samun yawancin masu kamuwa da ciwon a kasashen Afirka da na kudu maso gabashin Asiya. Galibin wadanda suka kamu da ciwon kan warke. Amma kalilan daga cikin masu kamuwa da ciwon kan dauki watanni ko shekaru da dama suna fama da ciwon gabobi.

Jami’ar ta kara da cewa, sakamakon dumamar yanayi a duniya, ya sa cututtukan da sauro ke haddasawa suna kara yaduwa a sassan duniya, inda ake samun masu kamuwa da cututtukan a arewacin kasashen Turai.

Jami’an WHO sun yi kira ga kasashen duniya, da su dauki matakan gaggawa na hana sauro yada cututtukan, da inganta sa ido kan cututtuka, a kokarin magance barkewar cututtukan a wurare da dama. (Tasallah Yuan)