WHO ta yi kira da a dauki matakan shawo kan hauhawar cutar daji a Afirka
2024-02-05 09:50:29 CMG Hausa
Ya kamata a ce karuwar yaduwar cutar daji a Afirka ta zama abin lura ga gwamnatoci don aiwatar da manyan matakai da za su rage yawan masu kamuwa da mace-mace, a cewar jami'ar hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO a jiya Lahadi yayin bikin ranar cutar daji ta duniya.
Matshidiso Moeti, darektar hukumar lafiya ta WHO a nahiyar Afirka, ta ce nahiyar na fama da matsalar ciwon daji da ke yin illa ga rayuwa tare da rage tsawon rayuwa, wadda ke bukatar hannun jari a matakan rigakafi da shawo kan matsalar.
Moeti ta bayyana cewa, mace-mace masu alaka da cutar daji a nahiyar za ta kai miliyan daya a duk shekara ya zuwa shekara ta 2030, inda ta kara da cewa, a cikin shekaru 20 masu zuwa, ana sa ran adadin wadanda za su mutu a dalilin cutar daji a Afirka zai zarce matsakaicin kashi 30 cikin dari a duniya.
Ta yaba da gagarumin ci gaban da kasashen Afirka ke samu wajen yaki da cutar daji, inda ta bayyana cewa, kasashe 17 sun riga sun gabatar da gwaje-gwaje masu inganci bisa ga shawarwarin WHO.
Bugu da kari, kasashe mambobin WHO 28 na Afirka sun bullo da allurar rigakafin cutar papillomavirus (HPV) a duk fadin kasar, wanda zai kai ga kusan kashi 60 cikin 100 na mutanen da aka yi niyyar yiwa rigakafin, ciki har da mata matasa, a cewar Moeti. (Yahaya)