logo

HAUSA

An gudanar da bukukuwan shagalin murnar bikin bazara na CMG a Habasha

2024-02-05 21:20:28 CMG Hausa

A ranar 3 ga wata bisa agogon wurin, an gudanar da taron masu wasanni na wucin gadi wato Flash mob, game da shagalin murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin mai taken “Gabatarwar murnar bikin bazarar gargajiya ta kasar Sin da kallon shagalin bikin bazara na CMG” a tashar Labu ta layin dogo na Addis Ababa zuwa Djibouti dake Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha. 

A dandalin Meskel da ke tsakiyar birnin Addis Ababa, an kuma nuna faifan bidiyo na tallata shagalin murnar bikin bazara na kasar Sin na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, wanda ya kawo yanayin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a Habasha dake gabashin Afirka. (Mai fassara: Bilkisu Xin)