logo

HAUSA

An shirya bikin murnar sabuwar shekara ta Sinawa dake tafe a Abujan Najeriya

2024-02-05 10:00:25 CMG Hausa

A yayin da ake shirin shiga shekarar dabbar Loong, bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, al'ummar Sinawa mazauna Najeriya, masu kaunar kiyaye da yada al'adunsu ga makwabta da abokansu na Najeriya, sun shirya shagulgula a Abuja, babban birnin kasar.

Wani injiniya dan Najeriya da ya halarci bikin na shekara-shekara a karon farko mai suna Adeshina Adegboye ya bayyana cewa, bikin tamkar wani taron al’adu ne dake kunshe da nau’ikan fasahohin al’ummar Sinawa.

Wannan shi ne karon farko cikin lokuta da dama, da aka zayyana bikin da aka fi sani da bikin bazara, wanda ya fado a ranar 10 ga watan Fabrairun wannan shekara.

Bikin wanda ofishin jakadancin Sin dake Najeriya da cibiyar al'adun Sin dake Abuja suka shirya, ya samu halartar dimbin jama'a, ciki har da daliban makarantun sakandare.

Mahalarta bikin da suka taru a cibiyar al'adun Sin da ke tsakiyar cibiyar kasuwanci a Abuja, sun ji dadin yadda aka nuna al'adun kasar Sin da kuma wasannin fasaha daban-daban na Sinawa da Najeriya.

Jama'ar da suka hada da Sinawa, da ’yan Najeriya, da na sauran kasashe, sun rungumi musayar al'adu, inda suka dauki wani babban hoto dake nuna alamar" hadin kai." (Ibrahim Yaya)