logo

HAUSA

Wannan takarda ta nuna tushen manufar kasar Sin

2024-02-05 15:35:36 CMG Hausa

sharhi na Bello Wang


Abokaina, a ganinku, me ya kamata a ce takardar farko da mahukuntan wata kasa su kan gabatar a duk shekara ta kunsa?

A kwanakin nan, kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da majalisar gudanarwar kasar suka gabatar da Takarda Mai Lamba 1 ta bana, wadda ta shafi ayyuka masu alaka da aikin gona, da raya kauyuka, gami da manoma. Shekaru 21 a jere ke nan da shugabannin kasar Sin suka gabatar da takarda ta farko a shekara da ta shafi wannan jigo.

To, sai dai me ya sa ake daukar aikin gona, da kauyuka, da manoma da matukar muhimmanci a kasar Sin?

Saboda da sai da aikin gona mai inganci ne ake iya tabbatar da cewa al'ummar kasar Sin fiye da biliyan 1.4 suke iya samun isasshen abincin da suke bukata. Kana kauyuka a nasu bangare, ba su kai birane a fannin ci gaban tattalin arziki ba, don haka dole ne a ba su karin tallafi. Yayin da ingancin rayuwar manoma ke zama wani muhimmin bangare da zai tabbatar da samun daidaito tsakanin al’umma, inda dukkansu za a wadatar da su a kasar ta Sin.

Wato ana mai da hankali kan aikin gona, da kauyuka da manoma a kasar Sin ne domin neman tabbatar da ci gaban kasa mai dorewa kuma cikin daidaito, da samun ingantuwar rayuwar jama'a a kai a kai. Sa’an nan tushen wadannan manufofi shi ne tunanin shugabannin kasar Sin na "Mai da jama'a gaban kome. "

Wannan tunani ya yi tasiri kan manufofin kasar Sin na cikin gida da na waje. Saboda haka gwamnatin kasar tana raya aikin gona, da harkoki masu alaka da kauyuka da manoma a cikin gida, gami da neman gina "al'ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya" a duniya, inda take kokarin haifar da ci gaba a sauran kasashe masu tasowa.

A kasar Sin, don ganin an tabbatar da samar da isashen abinci, ana ta kokarin fito da sabbin fasahohin aikin gona da za su tabbatar da samun girbi mai armashi a gonaki. Yayin da a jihar Morogoro ta kasar Tanzania, wasu kwararru Sinawa sun yi kokarin yada fasaha mai inganci ta shuka masara, cikin shekarun da suka gabata, inda har yawan masarar da ake girbi a can ya ninka sau 3.

Ban da haka, a lardin Zhejiang na kasar Sin da na taba ziyarta, na ga yadda kauyuka su ke raya sana'ar da ta dace da albarkatunsu. Misali a kan yi kiwon kifi a wuraren dake dab da tabkuna, da raya aikin yawon shakatawa a wurare masu duwatsu. Sa'an nan, a kasar Kongo Brazaville, ana yawan noman rogo, wanda yake lalacewa da wuri yayin da ake ajiyewa da jigilarsu. Saboda haka, bisa la'akari da yanayin da ake ciki wajen gudanar da aikin gona a Kongo Brazaville, da bukatar dake akwai, Sinawa sun samar da wasu injuna na sarrafa rogo, inda ake nika shi zuwa gari a kasar, matakin da ya taimaka wajen raya masana'antu, baya ga taimakawa manoma samun karin kudin shiga.

Haka zalika a wani kauye mai suna Ping Di Cun dake kudancin birnin Beijing na kasar Sin, na ga yadda gwamnatin wurin ta zuba kudade, tare da dasa itatuwa, da gina wuraren shakatawa, da sabbin ban dakuna, don inganta zaman rayuwar mazauna kauyen. Yayin da a Najeriya, wani kamfanin sadarwa na kasar Sin shi ma ya saukaka zaman rayuwar manoma, inda injiniyoyinsa suka yi amfani da itatuwa wajen kafa ginshikai masu dauke da na'urar samar da wutar lantarki ta hasken rana, da na'urorin sadarwa, ta yadda hakan ya taimaki mazauna kauyuka wajen magance matsalolin sadarwa, ban da wannan kuma, an ba su damar cajin wayoyin salularsu kyauta.

Bisa wadannan misalai muna iya ganin cewa, manufofin kasar Sin na cikin gida da na hulda da kasashen waje suna da tushe iri daya, wato tunani na mai da hakki da moriyar jama'a gaban kome. Wannan ma wani dalili ne da ya sa ake iya tabbatar da gaskiya, da kauna, da nuna sahihanci, gami da samar da hakikanin sakamako, yayin da ake gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. (Bello Wang)