logo

HAUSA

Shugaban Masar ya yi kira da a kafa kasashe biyu domin warware matsalar Falesdinu

2024-02-05 10:01:19 CMG Hausa

Shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi, ya jaddada bukatar sake farfado da shawarwarin kafa kasashen biyu, a matsayin tushen daidaita batun Palestinu, da maido da tsaro da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.

Fadar shugaban Masar ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa, shugaba Sisi ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawar da ya yi da ministan Faransa mai kula harkokin Turai da na ketare Stephane Sejourne.

Sanarwar ta ce, taron ya mayar da hankali ne kan kokarin Masar da bangarori daban-daban na ganin an tsagaita bude wuta a zirin Gaza, da samar da agajin jin kai don kawo karshen mummunan bala'in jin kai da al'ummar Gaza ke fuskanta.

Tattaunawar ta kuma jaddada wajibcin kasashen duniya, na daukar nauyin aiwatar da kudurorin da kasashen duniya suka cimma kan wannan batu.

Ministan na Faransa ya tabbatar da aniyyar kasarsa, na hada kai da Masar wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin da musayar fursunoni kamar yadda kasashen biyu suka yi imanin cewa, yana da muhimmanci a hana yaduwar rikicin.

A cewar sanarwar, bangarorin biyu sun kuma jaddada yin watsi da duk wani mataki ko manufofin dake da nufin korar Falesdinawa daga yankunansu.

Bugu da kari, sun jaddada muhimmiyar rawa da ma tasirin hukumar MDD dake samar da agaji ga 'yan gudun hijirar Falesdinu a yankin Gabas ta Tsakiya (UNRWA) wajen ba da taimako da agaji ga al'ummar Zirin Gaza. (Ibrahim Yaya)