logo

HAUSA

Farangiz, ‘yar kasar Uzbekistan: "Ina son wannan kasar Sin mai kuzari"

2024-02-05 17:12:43 CMG Hausa

Sun zo kasar Sin ne saboda sha'awarsu kan wannan kasa, kuma sun zabi zama a kasar Sin saboda cimma burinsu a nan. Lokacin da dalibai 'yan kasashen waje suke karatu da zama a kasar Sin, wadanne irin abubuwa za su ji? A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku wani labari ne game da labarin na wata baiwar Allah mai suna Farangiz, ‘yar kasar Uzbekistan dake karatu da kuma zama a nan kasar Sin.

Shugaban kasar Uzbekistan Shavkat Miromonovich Mirziyoyev, ya kai ziyarar gani da ido a kasar Sin daga 23 zuwa 25 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki. A cikin sharhin da ya rubuta, ya ce, "A duk lokacin da na ziyarci kasar Sin, ina nuna matukar jin dadina ga manyan nasarori da babban tasirin da kasar Sin ta samu wajen yin gyare-gyare da raya kasa." Ga Farangiz, wata daliba daga kasar Uzbekistan da ke zaune a kasar Sin, kasar Sin mai cike da kuzari ko da yaushe ta kan ba ta mamakin da ba ta taba gani ba.

Yin magana da Sinanci mai kyau, sanye da shudin rigar gargajiya ta kasar Sin, da kuma gashinta daure a bayan kanta……Duk wadannan abubuwa masu salon kasar Sin na dacewa sosai da Farangiz, 'yar kasar Uzbekistan.

Faranigzi ta ce, soyayyarta da sha'awarta ga kasar Sin sun fara ne tun tana karama.

“A lokacin da nake yar shekara bakwai zuwa takwas, yar inna ta da ta yi karatu a kasar Sin. Ta ba ni labarai da dama game da yadda tayi karatu da zama a kasar a wancan lokacin, wadanda suke da ban sha'awa kwarai.”

Tun daga wancan lokacin ne wani dan karamin iri na yin karatu a kasar Sin ya sami tushe kuma ya yi toho. Don cimma wannan buri, Faranigzi ta yi aiki tukuru don koyon Sinanci tun tana makarantar sakandare. A shekarar 2021, ta cimma nasarar shigar Jami'ar Minzu ta kasar Sin don neman digiri na farko a fannin Koyar da Sinanci ga masu magana da wasu harsunan waje.

A lokacin farko da ta iso birnin Beijing, ta yi mamakin ganin yadda kasar Sin ke cike da kuzari.

“Lokacin da na isa kasar Sin ne na fara haduwa da ganin birane na zamani dake da manyan gine-gine, manyan tituna, da kuma fasahohin zamani, duk suna da kyau sosai. Na kuma sadu da abokai da abokan karatu da yawa, Sinawa masu son juna da abokantaka, wadanda taimakonsu da goyon bayansu ya sa na ji dadi da kwanciyar hankali, wadannan abubuwan sun sa na kara son wannan kyakkyawar kasa."

A cikin hirar, Faranigzi ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen bayyana kaunarta ga kasar Sin da al'adun Sinawa cikin harshe irin na wakoki.

“Kasar Sin tana da ban sha'awa sosai, kuma tana burge ni sosai. Fadar Sarkuna ta Sin mai kyan gani da girma, da Dandalin Ibada na Sama mai natsuwa da ban mamaki, Fadar Shakatawa ta Sarkuna wato Summer Palace mai kyawawan yanayi, da kwararo da tsakar gida masu halin musamman, duk suna barin haske a cikin zuciyata.”

Faranigzi ta ce, tana matukar son wannan wurin, tana iya jin bugun kasar nan, hakan ya sa ta ji dadi da zumudi. A ganinta, hikimar mutane na kasar Sin a can can can da tana da ban girmamawa. Tana matukar sha'awar Tunanin Confucius, wanda ke jaddada dangantaka tsakanin mutane, kyautatawa da jituwa, da nanata 'kada ku yi wa wasu abin da ba ku so ku yi wa kanku', ta hakan ake iya ganin halin Sinawa na kasancewa mau mutunci da girmama mutane. Faranigzi ta kara da cewa, a kan hanyar samun wadata da karfi a kasar Sin, a koyaushe ana iya ganin goyon bayan da aka samu daga wajen al'adu.

Kasar Uzbekistan tana dab da cibiyar yankin tsakiyar Asiya, tana da dogon tarihi da yawan al’adun da aka gada daga kakani, da ma dimbin kayayyakin tarihi, ita ce babbar cibiyar tsohuwar hanyar siliki da kuma wurin da al'adu iri daban-daban ke haduwa.

A yau, bisa tsarin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Uzbekistan na kara habaka, kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na kara samun ci gaba da inganci, wanda ya sa Faranigzi ke sa ido ga makomar abokantaka tsakanin kasashen biyu a nan gaba.

“Shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ tana da matukar muhimmanci, kuma ita ce gadon abokantakar dake tsakanin kasashen biyu na dubban shekaru. Yanzu mun kuma bunkasa zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni kuma a duk wane halin da ake ciki a sabon zamanin. Ta fuskar tattalin arziki, ina fatan kasashen biyu za su iya fadada harkokin cinikayya, hakan za a iya kara gudanar da kasuwanci yadda ya kamata. Ta fuskar al'adu, ina fatan bangarorin biyu za su karfafa yin mu'amala da juna ta yadda al'ummomin kasashen biyu za su kara fahimtar juna. A fannin ilimi kuma, ina fatan kasashen biyu za su iya musayar albarkatu na ba da ilimi, da kuma karfafa hadin gwiwa wajen horar da kwararru da yawa. Ta haka, dangantakar dake tsakanin Sin da Uzbekistan za ta kara karko, da kuma kai ga samun wadata tare.”

A karshe dai, Faranigzi ta ce, ci gaban dangantakar da ke tsakanin Uzbekistan da Sin, ya sa ta samu karin zabi a rayuwarta, za ta yi aiki tukuru, kuma a matsayinta na matashiya za ta ba da gudummawa wajen sada zumunci tsakanin Uzbekistan da Sin.