logo

HAUSA

Ziyarar Faeza Mustapha a “Birni na kankara”

2024-02-04 22:15:21 CRI

Yanzu a nan kasar Sin, akwai wani birnin da yake matukar jan hankalin al’umma, sakamakon yadda dimbin masu yawon shakatawa ke tururuwa zuwa wajen tun bayan da aka shiga lokacin dari a bara. Sunan birnin kuma shi ne Harbin, wanda shi ne hedkwatar lardin Heilongjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin.

Muna iya gano haka ta bikin sabuwar shekara na farkon bana, a tsawon hutun bikin na kwanaki uku, birnin ya karbi masu yawon shakatawa da yawansu ya wuce miliyan uku, abin da ya samar masa kudin shiga kusan Yuan biliyan shida, kwatankwacin dala sama da miliyan 830, adadin masu yawon shakatawa da ma kudin shigar da ya samu duka sun zarce na shekarar 2019, har ya kai wani matsayin koli a tarihin birnin.

A kasance tare da mu cikin shirin Allah Daya Gari Bamban, don jin tattaunawarmu tare da malama Faeza Muhammad Mustapha dangane da ziyarar gani da ido da ta kai birnin na Harbin. (Lubabatu)