Jiragen yakin Amurka da Birtaniya sun kai hari kan sansanonin Houthi na Yemen
2024-02-04 09:45:25 CMG Hausa
Rahotanni daga Sanaa, babban birnin Yemen na cewa, sansanonin mayakan Houthi dake Sanaa sun fuskanci hare-hare ta sama jiya da dare.
Mazauna garin sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, hare-haren sun shafi sansanonin mayakan dake kewayen birnin Sanaa, kuma an ji dirin jiragen yaki da dama a cikin Sanaa, babban birnin kasar Yemen.
A cewar gidan talabijin na al-Masirah dake karkashin ikon mayakan Houthi, hare-haren ta sama sun sauka a kan tsaunin al-Nahdain da Attan, dukkasu sansanonin soji ne dake karkashin ikon kungiyar Houthi.
A halin da ake ciki kuma, tashar talabijin ta al-Masirah ta bayyana cewa, kasashen Amurka da Birtaniya sun kaddamar da hare-hare ta sama kan wasu wurare a babban birnin kasar.
Kawancen kasashen Amurka da Birtaniya ba su ce komai ba kan wadannan hare-hare. Sai dai kafofin yada labaran Amurka sun rawaito wasu jami'an sojin kasar da ba a bayyana sunayensu ba na cewa, sojojin Amurka sun kai hari kan 'yan Houthi sama da 30 a ranar Asabar a wurare daban-daban na kasar Yemen, ciki har da babban birnin kasar Sanaa. Jami’an sun yi ikirarin cewa, hare-haren ta sama da aka kai, na daga cikin martani kan harin da jiragen yaki mara matuki da mayakan na Houthi suka kai, wanda ya kashe sojojin Amurka uku a Jordan a makon jiya.
Wannan shi ne farmaki na hudu da kawancen da Amurka ke jagoranta kan cibiyoyin mayakan Houthi cikin kasa da sa'o'i 24. (Ibrahim Yaya)