logo

HAUSA

Shugaban Namibiya Geingob ya rasu a asibiti

2024-02-04 16:46:51 CMG Hausa

Rahotanni daga fadar shugaban kasar Namibia na cewa, shugaban kasar Hage G. Geingob ya rasu a safiyar Lahadin nan a wani asibitin dake Windhoek, babban birnin kasar.

Mukaddashin shugaban kasar Nangolo Mbumba, ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya wallafa a shafin sada zumunta na fadar shugaban kasar cewa, “a cikin tsananin bakin ciki da nadama, ina sanar da ku cewa, masoyinmu Dr. Hage G. Geingob, shugaban kasar Namibiya, ya rasu yau Lahadi 4 ga Fabrairu 2024 da misalin karfe 12 da mintuna 4 na safe, a asibitin Lady Pohamba inda yake samun kulawa daga tawagar likitocinsa.”

Sanarwar ta ce, tawagar likitocinsa sun yi iyakacin kokarinsu don ganin cewa shugaban namu ya murmure, sai dai abin takaici, duk da kokarin da likitocin suka yi na ceton rayuwarsa, abin bakin ciki, 'yan kasar Namibiya, shugaba Geingob ya rasu.

A ranar Asabar, mataimakin shugaban kasar Mbumba ya shaidawa al'ummar kasar cewa, shugaba Geingob na cikin wani mawuyacin hali, amma ya samu sauki, bayan da aka yi masa maganin cutar kansa a asibitin Lady Pohamba dake Windhoek, babban birnin kasar.

A ranar 19 ga watan Janairu, fadar shugaban kasar Namibiya ta ce, tawagar likitocin Geingob sun gano kwayoyin cutar daji, bayan wani binciken lafiya da aka yi masa. (Ibrahim Yaya)