logo

HAUSA

CMG ya shirya gabatarwa game da shagalin murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin a Brazil

2024-02-04 21:37:30 CMG Hausa

Jiya Asabar ranar 3 ga wata bisa agogon wurin a Recife na kasar Brazil, aka gudanar da bikin musamman na Brazil mai taken “Gabatarwar murnar bikin bazarar gargajiyar kasar Sin da kallon shagalin bikin bazara na CMG”, wanda karamin ofishin jakadancin kasar Sin a Recife da ofishin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin(CMG) dake Latin Amurka suka shirya tare.

Birnin Recife, wani muhimmin gari a arewa maso gabashin Brazil, ya zartar da wata doka a shekarar 2022, inda aka yanke shawarar ayyana bikin bazara na kasar Sin a matsayin bikin birnin a hukumance. Tun daga wancan lokacin, Recife ya zama birni na farko a Brazil dake gudanar da bikin bazara na kasar Sin a hukumance, wanda ke nuna cikakken dankon zumuncin dake tsakanin jama'ar Sin da Brazil.

Shekarar 2024 ta dabbar Dragon ta kasar Sin ta zo daidai da cika shekaru 50 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Brazil. A wurin gudanar da bikin, an nuna tambarin da kasashen biyu suka tsara don murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu. Lamarin da ya nuna cewa, a ko da yaushe kasashen biyu na mutunta juna, da daukar junansu bisa daidaito, da kuma yin hadin gwiwa don samun nasara tare, tun bayan kulla huldar diflomasiyya na tsawon rabin karni. (Mai fassara: Bilkisu Xin)