logo

HAUSA

Iraki ta nuna adawa a hukumance da hare-hare ta sama da Amurka ke kaiwa a wasu sassan kasar

2024-02-04 10:53:19 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta gayyaci jami'in diflomasiyar Amurka dake Iraki jiya Asabar, don nuna adawa da hare-hare ta sama da Amurka ta kai kan wasu wurare a Iraki.

Ma'aikatar harkokin wajen Iraki ta fitar da sanarwa a wannan rana inda a ciki ta yi Allah wadai da harin da jiragen yakin Amurka suka kai kan cibiyoyin tsaron Iraki.

Iraki ba dandali ne da manyan kasashen duniya za su gudanar da gwagwarmayar siyasa ba, kuma ba wuri ba ne inda wasu bangarorin da abin ya shafa, ke aika sakonni ko nuna karfinsu. Gwamnatin Iraki za ta sauke nauyin da tsarin mulki ya dora mata, kare ikon mallakar kasa, da kiyaye rayukan jami’an tsaro da na fararen hula. (Safiyah Ma)