logo

HAUSA

Sin Ta Gabatar Da Taswirar Raya Kauyuka Cikin Takarda Mai Lamba 1 Ta Kwamitin Tsakiya Ta 2024

2024-02-04 23:20:22 CMG Hausa

Jiya Asabar, an gabatar da takarda mai lamba 1 wadda ke da nasaba da aikin jagorar ayyukan raya kauyuka da manoma da aikin gona. Wadda ta zayyana jerin matakan da za a bi don inganta farfado da yankunan karkara.

A matsayin ta na sanarwar manufofi ta farko da gwamnatin kasar Sin take fitarwa a kowace shekara, ana daukar takardar a matsayin wata babbar alamar manyan manufofin gwamnatin kasar.