logo

HAUSA

An kashe mutane 16 a harin da jiragen yakin Amurka suka kai a yammacin Iraki

2024-02-03 20:24:27 CMG Hausa

Gwamnatin Iraki ta fada a yau Asabar cewa, harin da jiragen yakin Amurka suka kai kan sojojin Hashd Shaabi dake yammacin kasar Iraki ya kashe mutane 16 da suka hada da fararen hula tare da jikkata wasu 25.

Kakakin gwamnatin kasar Basim al-Awadi ya ce harin da jiragen suka kai ta sama “babban ta’adi ne”, ya kuma shaidawa kamfanin dillancin labaran Iraki (INA) cewa, gwamnatin Amurka ta keta ‘yancin kasar Iraki.

A gefe guda kuma, a ranar Asabar har ila yau, kasar Syria ta yi Allah-wadai da hare-haren da Amurka ta kai a baya-bayan nan kan mayakan sa-kai masu goyon bayan Iran a cikin kasar, tana mai cewa harin da nufin gurgunta yakin da kasar Syria ke yi da ta'addanci. (Yahaya)