logo

HAUSA

CMG ya shirya shagali gabanin liyafar bikin bazara a Geneva

2024-02-03 15:20:17 CMG Hausa

A jiya Juma’a ranar 2 ga wannan wata ne rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin ko CMG a takaice ya shirya shagali gabanin liyafar bikin bazara mai taken “Taya murnar bikin bazarar gargajiyar kasar Sin ta hanyar kallon liyafar bikin bazara ta CMG” a ofishin MDD dake birnin Geneva na kasar Switzerland, inda aka samu halartar bakin da suka zo daga ofishin MDD dake Geneva, da kungiyoyin kasa da kasa sama da 300. Makasudin shirya shagalin shi ne habaka cudanyar al’adu tsakanin kasa da kasa ta hanyar nuna al’adun bikin bazara na gargajiyar kasar Sin.

Kana a wannan rana an shirya bikin musamman mai taken “Magajin Loong na taya murnar shekarar Loong” kan liyafar bikin bazara ta CMG a lambun shan iska na hasumiyar Burj Khalifa dake Dubai.

Hakaza lika, tasha ta biyu ta gidan rediyo da talibijin na kasar Italiya ta gabatar da shirin bidiyon dandanon liyafar bikin bazara ta CMG, inda aka yi bayani kan sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, shirin da ya kasance karon farko da aka gabatar game da liyafar bikin bazara na kasar Sin a gidan rediyo da talibijin a kasar Italiya. (Jamila)