logo

HAUSA

Faraministan Nijar na ziyarar aiki ta kwanaki uku a kasar Turkiyya

2024-02-03 14:48:04 CGTN HAUSA

Faraminstan Nijar Ali Mahamane Laine Zeine na cikin ziyarar aiki ta kwanaki uku da ya fara a ranar 31 ga watan da ya gabata. Shugaban gwamnatin Nijar ya yi amfani da wannan rangadi domin karfafa hulda da tsai da wata sabuwar dangantaka mai armashi da karko, a cewar fadar faraminstan Nijar.

Daga birnin Yamai, abokin aikimu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.