logo

HAUSA

Shugaba Bola Tinubu ya koka kan yadda ake zargin Najeriya a mastsayin kasa da ake yawan aikata laifuka ta kafar Intanet

2024-02-02 13:39:26 CMG Hausa

 

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana damuwa bisa yadda ake yawan zargin ’yan kasar da laifukan da suke da alaka da kafar Intanet da sauran ayyukan cin hanci da rashawa, zargin da ya bayyana dacewa ko kadan babu sahihanci a cikinsa .

Shugaban ya bayyana hakan ne a birnin Abuja yayin taron matasa da sarakuna da shugabannin addinai a game da yaki da cin hanci da zumma ta hanyar yanar gizo wanda hukumar EFCC ta shirya .

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Sanata Kashim Shettima ya zargi mutanen da suke yi wa Najeriya irin wannan mummunan kallo da cewa ba su yi kwakkwaran binciken da ya kamata ba kafin su fito da sakamakon rahoton.

Yayin taron wanda ya kunshi masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban na yaki da laifukan tattalin arziki da na kudi, har’ila yau an kaddamar da littafin da ya kunshi tsokacin masana a bangarorin addinai daban daban game da hadarin dake tattare da zamba ga ma’aikatu da sauran sassa da hukumomin gwamnati.

Shugaban kasar ya ce, ya yi mamakin ganin shekaru masu yawa ana alakanta daukacin ’yan Najeriya da laifukan intanet ba tare da hujja kididdigagga ba. Al’ummarmu tana kunshe ne da mutane hazikai masu aiki tukuru cikin gaskiya wadanda ke ba da gudummawa sosai a bangarori daban daban na ilimin kimiyya da fasaha a duniya.

“Ko da yake wajibi ne mu yarda cewa yanzu duniya na cike da kalubalen laifukan daban daban da ake aikata su ta kafar intanet, kuma a sabo da haka wannan matsala ba Najeriya kawai ta shafa ba, ta shafi duniya ne baki daya. Mun fahimci cewa kokarin da hukumar EFCC ke yi na yi amfani da doka domin hukunta ’yan damfara abu ne mai muhimmancin gaske ga rayuwar al’umma baki daya.”

Sanata Kashim Shettima, a madadin shugaban tarayyar Najeriya ya tunatar da matasan kasar cewa, akwai ayyukan yi a halak sosai a ciki da wajen kasar, wanda ya kamaci su yi kokarin yi maimakon mayar da hankali wajen mallakar kudi ta hanyar haram. (Garba Abdullahi Bagwai)