Tabbas Philippines ba za ta yi nasara a yunkurinta na kafa “karamar da’ira” a tekun kudancin kasar Sin ba
2024-02-02 19:21:44 CMG Hausa
Kwanan nan ne shugaban Philippine Marcon Marcos ya kammala ziyararsa a Vietnam. A yayin ziyarar tasa, ya yi ikirarin cewa, takaddamar ‘yanci tsakanin Philippines da kasar Sin “babu dadi.” Yayin da wasu kafofin watsa labarai na kasashen yammacin duniya ke ci gaba da ba da hadin kai wajen rura wutar husuma game da tekun kudancin kasar Sin tare da wuce gona da iri kana bin da suke kira “barazanar kasar Sin”
A cewar rahotannin, gwamnatocin Philippines da Vietnam sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyi biyu na fahimtar juna don kafa kwamitin hadin gwiwa na tsaron gabar teku. Masana sun ce, Philippines na son yin amfani da batutuwan tsaro wajen "kulla abota" da nufin yin fito-na-fito da kasar Sin a tekun kudancin kasar Sin, da kuma kara matsin lamba kan kasar Sin. Wannan wani sabon salo ne na Philippines kan batun tekun kudancin China.
Tsibiran Huangyan da Ren'ai yankunan gado ne na kasar Sin. A cikin shekarun da suka gabata, kasar Sin ta nuna matukar kiyayewa da hakuri. Yanzu, Philippines na ci gaba da yin kasada da kuma kokarin kara ta'azzara batutuwan da suka shafi kasashen biyu, wadanda za su cutar da muradunta na dogon lokaci kawai. (Yahaya)