logo

HAUSA

Wakilin Sin: ya kamata a tsagaita wuta tsakanin Falasdinu da Isra'ila nan da nan

2024-02-01 14:40:45 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya yi kira ga kwamitin sulhu da ya yi kokarin ganin an tsagaita wuta tsakanin Falasdinu da Isra’ila a jiya Laraba, a sa’i daya kuma ya yi kira ga kasashen duniya da ta nuna goyon baya ga Falasdinu wajen zama cikakkiyar mambar MDD, da ci gaba da goyon bayan aikin hukumar MDD mai ba da agaji ga ’yan gudun hijira na Falasdinu a yankin gabas ta tsakiya wato UNRWA a takaice.

Yayin da yake jawabi a taron bainar jama’a na kwamitin sulhun MDD kan batun Falasdinu da Isra’ila, Zhang Jun ya bayyana cewa, kasar Sin na nuna goyon baya matakan da kwamitin sulhu ke dauka wajen kawar abubuwan dake kawo cikas ga ayyukan jin kai. Ya ce, kotun hukunta manyan laifuffuka ta duniya, ta ba da umarni na wucin gadi a makon da ya gabata, wadanda ya kamata a hanzarta aiwatar da su yadda ya kamata. 

Kasar Sin ta ba da shawarar kiran babban taron zaman lafiya na kasa mai fa’ida da inganci, tare da tsara jadawalin aiwatar da shirin nan na kafa “kasashe biyu”.

Kasar Sin tana goyon bayan Palesdinu ta zama cikakkiyar mamba a MDD. (Safiyah Ma)