logo

HAUSA

Bach ya yi imanin cewa CMG zai yi ingantaccen aiki game da wasannin Olympics na Paris

2024-02-01 20:41:40 CMG Hausa

A ranar 31 ga Janairu ne a yayin gasar wasannin Olympics na matasa na lokacin sanyi da aka gudanar a Gangwon na Koriya ta Kudu, shugaban kwamitn wasannin Olympics na kasa da kasa Tomas Bach, ya yi wata hira da manema labarai na CMG a Gangling na kasar Koriya ta Kudu.

Bach ya ce za a gudanar da gasar Olympics ta birnin Paris a bana, kuma CMG za ta aike da tawagarta masu aikin dauka da yada shirye-shirye da ta kunshi kusan mutane 2000. Bach ya tabbatar da ingancin aikin CMG a baya game da wasannin Olympics, kuma yana da kwarin gwiwa kan rawar da CMG zai taka a gasar Olympics ta Paris. Ya ce, "Mun yi imanin cewa za ku gudanar da aikinku bisa tsarin inganci da kuka kafa a Paris." (Yahaya)