logo

HAUSA

AFCON 2023: Yadda Manyan Kasashe Ke Tafka Abin Kunya

2024-02-01 18:58:19 CRI

 

Cin kofin nahiyar Afirka gasa ce wacce manyan kasashe suka mamaye shekara da shekaru wajen yawan lashe kofin da kuma yin kokari tun daga farkon gasar har zuwa karshe, sai dai a wannan shekarar ta 2024, ana ganin abin mamaki domin yadda manyan kasashen suke nuna abin kunya sannan kananan kasashe suke ba wa mutane mamaki, yana nuna cewa tabbas kwallon kafa tana canjawa, kuma irin canjin da ya kamata a ce ana gani a wannan nahiyar ta Afirka.

Manyan kasashe ne suka mamaye yawan lashe gasar tun farkon farawa a shekarar 1957 inda kawo yanzu kasar Masar ta lashe gasar sau bakwai, sai kasar Kamaru wadda ta lashe sau biyar sai Ghana mai guda hudu, Nigeria kuma mai guda uku, sannan Kasar Ibory Coast, wadda take karbar bakuncin gasar a wannan lokacin mai guda biyu.

Hakan yana nufin manyan kasashen nahiyar Afirka su ne suka mamaye gasar wajen yawan lashewa, amma wannan gasar ta shekara ta 2024 ta zo da abin mamaki kuma masu sharhi akan gasar ta bana suna ganin za’a iya samun canji ganin yadda manyan kasashen suke yin tuntube.

Mai masaukin baki, Ibory Coast na dab da bankwana da gasar, bayan da Ekuatorial Guinea ta dura mata 4-0 ranar Litinin 22 ga watan Janairu, kuma wasa na uku a rukunin farko da suka buga kenan, inda Ekuatorial Guinea ta hada maki bakwai, ita kuwa Ibory Coast maki uku ne da ita sai, Nijeriya ita ma mai maki bakwai wadda take mataki na biyu a cikin rukunin.

 Ibory Coast za ta iya fitowa daga cikin rukuni duk da haka amma za ta jira ko za ta samu zuwa mataki na biyun, bayan da za a dauki tawaga hudu, wadanda suka yi na uku da maki mai yawa saboda tawaga biyu ce daga kowanne rukuni za ta kai zagayen gaba kai tsaye, yayin da za a hada da hudun da suka yi na uku a rukuni, amma wadanda suka hada maki mai yawa.

 

Wani abin mamaki shi ne bajintar da kasar Cape Berde take yi a gasar, duk da cewa ta fito a cikin rukunin da ya hada kasashen Ghana da kasar Masar da kasar Mozambikue kuma a yanzu haka kasar ta Cape Berde ita ce take jan rukuni na biyu bayan ta hada maki bakwai, sai kasar Masar ta biyu da maki uku, sai Ghana da tuni ta fice daga gasar da maki biyu.

 Tabbas abin mamaki ne a ce Ghana ta fice daga gasar cin kofin nahiyar Afirka a cikin rukuni kuma ta hada maki biyu kacal cikin maki tara da ake ganin za ta iya hadawa kafin fara gasar.

Sai dai tuni hukumomi a kasar ta Ghana suka sanar da korar kociyan tawagar, Chris Hughton, dan Ingila, wanda a baya ya taba koyar da kungiyoyin Newcastle United da Brighton. Har ila yau, hukumar dake kula da kwallon kafa ta Ghana ta sallami ragowar masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafar kasar, sannan nan gaba a cewar su, za su sanar da mataki na gaba da gwamnatin kasar za ta dauka a kan babbar tawagar kasar ta Ghana.

Babban abin mamakin dai shi ne kasar Ibory Coast, kasa mai masaukin baki, wadda ake ganin tana daya daga cikin manyan kasashen da za su iya lashe gasar saboda karfin tawagar sannan bugu da kari a kasar ake bugawa.

Ita ma tawagar ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya, duk da cewa ta samu tsallakewa zuwa mataki na gaba, amma masu sharhi kan wasanni suna ganin akwai babban aiki a gaban Nijeriya musamman wajen zura kwallo a raga.

 Cikin wasanni uku da Nijeriya ta buga kwallaye uku kacal ta zura a raga, sannan a cikin guda ukun, kwallo guda daya ce kawai Nijeriya ta zura ana cikin wasa domin kwallo daya da bugun fanareti Nijeriya ta zura sai kuma kwallo daya da dan wasan Guinea-Bissau ya ci gida, abin da ake kira da “Own Goal” da turance.

Ita ma Kasar Masar ba ta tabuka abin arziki a gasar ta ba na ba, domin a cikin wasanni uku da kasar ta fafata, ba ta samu nasarar lashe wasa ko guda daya ba, duka wasanninta canjaras ta buga wanda hakan ya sa ta hada maki uku kuma take mataki na biyu a cikin rukunin.

Duk da cewa Senegal ta samu damar tsallakawa matakin wasannin sili daya kwale tun a Juma’ar da ta gabata, amma a wasan da ta fafata ranar Talata tsakaninta da Guinea, ta yi nasara ne da kwallaye 2 da nema wanda ya bata damar kara yawan makinta zuwa 9.

Cikin dukkanin kasashen da suka tsallaka matakin na ‘yan 16 zuwa yanzu dai Ekuatorial Guinea, Najeriya da kuma Cape Berde ne kadai suka kusan kamo Senegal a yawan makin inda dukkaninsu suke da maki bakwai-bakwai.

Yayin da kasashe irinsu Masar suka taki sa a domin kuwa ta zama kasa mafi karancin maki da ta yi nasarar tsallakawa matakin ‘yan 16, lura da cewa ta na da maki 3 ne cal a wasanni 3 da ta buga wanda dukkaninsu ta yi canjaras, ba nasara ba kuma shan kaye.

A daya wasan da aka yi kuwa, Kamaru ta sha da kyar wajen samun gurbi a zagayen kasashe 16 na gasar cin kofin Afrika, bayan nasara kan Gambia da kwallaye 3 da 2 wanda ya ba ta damar kammala wasanninta na rukuni a matsayin ta 2 amma maki guda ita da Guinea wadda ta kammala a matsayin ta 3.

Wannan ne kadai wasan da Kamaru ta iya nasara cikin wasanni 3 da ta doka, wanda ke nuna ita da Guinea wadda ta kammala wasannin rukunin na B a matsayin ta 3 dukkaninsu sun yi nasara a wasa guda ne sun yi canjaras a guda sun kuma sha kaye a guda.

Kafin dai nasarar ta Kamaru, sai da alkalin wasa ya soke kwallo guda da Gambia ta ci, lokacin ana kwallo 3 da 3 kenan tsakanin bangarorin biyu gab da tashi daga wasa, wadda alkalin wasan ya bayyana da ta satar fage.

Duk da cewa Kamarun ta tsallake, amma ita ma Guinea ta yi zaman jiran tsammanin iya shiga sahun kasashen da suka kammala a matsayin na 3 mafiya maki, wato irin dai gurbin da mai masaukin baki Ibory Coast ta jira.

Ibory Coast wadda ke matsayin ta 3 a rukunin A ta kammala ne da maki 3 yayin da bayan nasara a wasa 1 tal da kuma kaye a wasanni 2, wanda ke nuna cewa Guinea na gabanta a yawan maki, domin kuwa ita ta na da maki 4 ne.