Kwadon Baka: Neman Dabbar Loong
2024-02-01 09:07:10 CMG Hausa
Bikin Bazara, biki ne da kashi 1 bisa 5 na al’ummu a fadin duniya ke murnarsa, kuma shi ne biki mafi girma ga Sinawa a duk shekara. Shirin Kwadon Baka ya zo gundumar Yu ta lardin Hebei na Sin, don mu kalli yadda ake murnar sabuwar shekara ta kasar Sin, ta hanyar amfani da wukar sassaka da bakinta ke da fadin milimita 1, da ruwan karfe mai zafin digiri 1600.